Buhari Ya Kamata Ya Jagoranci Nemo ?aliban Da Aka Sace – PDP

Babban jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya katse hutun da ya ke gudanarwa domin bin sahun yara daliban da aka sace a makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a taron manema labarai a Abuja, sakataren watsa labaran jam’iyyar na kasa Kola Ologbondiyan ya ce Buhari ne ya kamata ya jagoranci ceto daliban da aka sace a cikin makarantar.

A daren Juma’a ne ‘yan bindiga suka afka cikin makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara jihar Katsina suka kora dalibai da dama. Sai dai, wasu bayanai daga ma’aikatar ilmi ta jihar Katsina da rundunar ‘yansandan jihar Katsina, sun ce an gano wasu daga cikinsu.

Shugaban kasa Buhari dai na cigaba da fuskantar matsin lamba a gida da waje dangane da halin da rashin tsaro ya shiga a yankin Arewa, inda wasu ke kiran Shugaban da ya yi gaggawar yin murabus saboda gazawar shi a fili.

Related posts

Leave a Comment