Buhari Ya Kafa Tarihi Na Shugaban Da Aka Fi Zubar Da Jini A Mulkinsa – Birtaniya

A yayin da ake shirin tunkarar babban za?en a watannin farkon shekara mai zuwa lokaci yana kurewa wajen tabbatar da an yi za?en lami lafiya kuma da inganci, a cewar wani rahoto da cibiyar Tony Blair dake Birtaniya ta fitar.

Cibiyar ta Burtaniya ta yi tsokaci kan irin barazanar da za?en ke fuskanta kan irin yadda za?en zai iya samun cikas daga rikicin Boko Haram, da masu fafutukar a-ware ta haramtacciyar ?ungiyar IPOB.

Akwai kuma kungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan bangar siyasa da kuma masu ya?a labaran karya a shafukan sada zumunta da muhawara.

Cibiyar tayi tsokaci kan mahukuntan Najeriya da kawayenta na ketare kan daukan matakan tabbatar da cewa an yi za?e mai zuwa na shugaban ?asa da mataimaki da sanatoci da ‘yan majalisa da gwamnoni cikin kwanciyar hankali da sahihanci.

Cibiyar ta ce yin za?e cikin kwanciyar hankali zai kafa tarihi irin na dimokura?iya, shekara 24 bayan komawa ?asar tafarkin dimokuradiya.

Amma za?en da ke zuwa ko rigingimu ke mamayewa, ko wanda ake da shakku kan sahihancinsa, zai kasance babbar barazana da abin alla-wadai ga kasa da ke cikin kangin barazanar tsaro, rarrabuwar kawuna da matsalolin tattalin arziki.

Sai dai har yanzu ana iya daukan masu muhimmanci musamman ga wadanda hakkin tsaron kasa ya rayata wuyansu, da kuma tafiyar da harkokin za?en.

Cibiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta habbaka kokarinta wajen ‘yantar ko kare ?auyuka da garuruwa da hare-haren ‘yan ta’adda ke shafa kafin lokacin za?uka.

Akwai kuma bukatar tabbatar da cewa an tura jami’an tsaro domin sa ido kan za?ukan da cigaba da mur?ushe duk wani ko ?ungiyoyi masu hassada husuma.

Tabbatar da hukunta wadanda aka samu da laifukan za?en – ya?a labaran boge – zai kasance jan-kunne ga duk wanda yake da tunanin zagon kasa ko tada husuma ga tsarin dimokura?iya.

Rahoton ya kuma ce akwai bukatar dole ?asashen ?etare su marawa Najeriya a wannan yanayi mai matu?ar wahala.

Rahoton ya ta?o ?asashen Amurka da Burtaniya da Tarayyar Turai da su aike sakonni garga?i da goyon-bayan sahihin za?e da matsa lamba kan manyan kamfanonin fasaha su sanya ido kan shafukansu domin da?ile yada labaran boge ko ?arya.

Rahoton na musamman da aka aikewa BBC ya nuna cewa asarar rayuka mafi yawa da aka tafka a lokacin za?e shi ne 2011, da mutum 800 suka rasa rayukansu.

Sai kuma a 2007 da rigingimun za?e suka yi sanadin rayuka 300, sai kuma a 2019 mutum 145 da 2015 mutum100.

A cewar rahoton, a tsawon mulkin Shugaba Buhari daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2022, mutum 55,430 suka mutu a hare-haren ta’addanci da ‘yan fashi a fa?in ?asar.

A za?en 2003, mutum 100 suka mutu yayinda a 1999 lokacin da ?asar ta koma tafarkin mulkin dimokura?iya mutum 80 ne aka kashe a lokacin za?e.

Bincike ya nuna cewa lokacin da aka fi tafka asarar rayuka shi ne bayan za?en 2011, lokacin da aka yi tsanmanin cewa shugaban mai ci a yanzu shi ne ya yi nasara.

A wannan lokaci bayan sanar da cewa babban abokin hamayya a wannan lokaci, Buhari ya fa?i za?e, an shafe kwanaki uku ana tafka rikicin da ya yi sanadin rayuka 800, sannan dubu 65,000 suka rasa muhallansu.

Duk da cewa babu takardu ko bayanai da ke kunshe da bayanan rikici da aka yi a 2015 da 2019, masu sa ido kan za?e na Tarayyar Turai sun ce rikici da tsangawama ya mamaye za?en 2019, inda “jami’na INEC da masu ka?a kuri’a suka rinKa fuskantar barazana daga magoya-bayan jam’iyyu”.

EU ta bada rahoton cewa a?alla mutum 145 aka kashe a rikicin da ke da ala?a da za?e a 2019, adadin da ya haura abin da aka gani a za?en 2015, na mutum 100.

A za?en 2019, manya ‘yan takara, Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar, dukkaninsu Fulani ne kuma Musulmai daga Arewacin Najeriya, abin da ya rage tashin hankali a wannan lokaci.

Hakazalika, a 2015, amsa shan kaye da tsohon Shugaba Jonathan ya yi tun kafin a bayyana sakamakon karshe ya taimaka wajen kaucewa sake maimaita abin da ?asar ta gani a za?en 2011.

Sai dai a manyan masu takara a za?en shugaban kasa na 2023, Tinubu da Atiku, duk Musulmai ne, kabilarsu ba ?aya ba hakazalika yankin da suka fito kamar lokacin Buhari da Atiku.

Sannan wani abin la’akari shi ne, za?en da ke tafe akwai karin ‘yan takara biyu masu karfi, Peter Obi, Kirista daga Kudu maso gabashi, da Rabi’u Kwankwaso, Musulmi daga Arewa maso yamma, dukkaninsu na da magoya baya masu karfi.

Masu sa ido na ganin dole a lalubo hanyar tabbatar da zaman lafiya tsakanin wadannan ‘yan siyasa domin mutunta sakamakon za?e, domin tun yanzu ana hasashen abubuwa da dama zasu biyo bayan za?en 2023 kusan makamancin abin da aka gani a 2011.

Related posts

Leave a Comment