Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Ya Isa Chadi Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya isa ?asar Chadi a ranar Litinin don halartar rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin ri?on ?warya ta Jamhuriyar Chadi na tsawon shekara biyu.

An yi bikin rantsuwar ne a N’Djamena, babban birnin ?asar, inda aka tattauna kan batun mayar da ?asar turbar dimokradiyya, bayan mutuwar tsohon shugaban Idriss Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, wanda aka kuma sani da Mahamat Kaka, ?a ne ga marigayi shugaban Chadin Idris Deby.

A wata sanarwa mai ?auke da sa hannun Garba Shehu, mai taimaka wa Buhari kan ya?a labarai, ta ce shugaba Buhari zai dawo Najeriya bayan kammala rantsarwar.

Exit mobile version