Buhari Ya Isa Chadi Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya isa ƙasar Chadi a ranar Litinin don halartar rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Jamhuriyar Chadi na tsawon shekara biyu.

An yi bikin rantsuwar ne a N’Djamena, babban birnin ƙasar, inda aka tattauna kan batun mayar da ƙasar turbar dimokradiyya, bayan mutuwar tsohon shugaban Idriss Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, wanda aka kuma sani da Mahamat Kaka, ɗa ne ga marigayi shugaban Chadin Idris Deby.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Garba Shehu, mai taimaka wa Buhari kan yaɗa labarai, ta ce shugaba Buhari zai dawo Najeriya bayan kammala rantsarwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply