Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP reshen Kudu maso Gabashin Nijeriya ta ce shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya gaza wajen sauke manyan al?awuran da ya yi, da suka ha?a da inganta tsaro, ?arfafa tattalin arzi?i da ya?i da cin hanci.
Sakataren ya?a labaran jam’iyyar na shiyyar, Elochukwu Okeke ya fa?i haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
A cewar PDP, Nijeriya ta dawo kasa mafi talauci a duniya, ?aya daga cikin ?asashen da ayyukan ta’addanci suka ta’azzara a duniya da kuma samun yara masu yawa da ba su zuwa makaranta a lokacin mulkin Buhari.
Jam’iyyar adawar ta ce tuni Nijeriya ta sauka daga al?alumman auna ?wazon ya?i da cin hanci na ‘Transparency International’ wanda hakan ya sa ?asar ta kasa ya?i da cin hancin.
Martanin jam’iyyar PDP ?in na zuwa ne kwana guda da shiga sabuwar shekara ta 2021 bayan da Shugaba Buhari ya gabatar da jawabin shi ga ‘yan Najeriya, inda ya bugi kirji da cewar gwamnatin shi ta yi rawar gani.