Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan tafiyar da ya yi domin duba lafiyarsa a Birtaniya.
A wani saƙo da mataimakin shugaban na musamman kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi da maraice ya ce shugaban ya sauka a Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban ya kwashe kusan makwanni biyu a birnin Landan, bayan da ya bar ƙasar ranar 31 ga watan Oktoba domin a duba lafiyarsa.
A lokacin bulaguron nasa Shugaban Buhari ya ziyarci sarki Charles lll a fadarsa da ke Buckingham.
Bincike ya nuna cewa ya zuwa watan Disamba a shekarar 2021, shugaba Buhari ya yi tafiya akalla sau tara zuwa kasashen waje. Duk da cewa a baya fadar shugaban kasar ta bayyana wadannan tafiye-tafiyen a matsayin masu muhimmaci, ‘yan Najeriya da dama sun ce shugaban zai iya tura wakilai.
Yawancin ‘yan kasar na da ra’ayin cewa hakan zai rage kashe kudi da kuma ba Buhari karin lokaci domin halartar muhimman batutuwan da suka shafi kasa.
A duk lokacin da Buhari ya yi irin wadannan tafiye-tafiye, yakan tafi tare da rakiyar jami’an gwamnati da suka hada da masu daukar hoto, jami’an tsaro, da mataimakansa a harkokin yada labarai daban-daban.
Ga jerin tafiye-tafiyen da shugaban kasar ya yi zuwa kasashen duniya a shekarar 2021.
-Burtaniya karo na farko A ranar 30 ga watan Maris ne shugaba Buhari ya tashi zuwa birnin Landan domin duba lafiyarsa kuma ya dawo mako na biyu na watan Afrilu. Wannan ita ce ziyarar jinya ta farko da shugaban na ya kai kasar waje tun bayan barkewar cutar Korona.
A watan Yuli, shugaban ya sake tafiya Landan, wannan lokacin don halartar taron koli na Ilimi na Duniya na GPE 2021-2025. Bayan kammala taron ilimi Buhari ya shafe lokaci a Landan domin duba lafiyarsa. Ya dawo mako na biyu na watan Agusta.
-Kasar Amurka: A watan Satumba, shugaba Buhari ya halarci taro na 76 na Majalisar Dinkin Duniya (UNGA76). Ya yi jawabi ga shugabannin kasashen duniya a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, inda ya yi jawabi kan taken taro da sauran batutuwan duniya.
-Kasar Habasha: A farkon watan Oktoba shugaba Buhari ya je kasar Habasha inda ya halarci bikin rantsar da Firayim Minista, Abiy Ahmed. Buhari wanda ya bar Abuja zuwa babban birnin kasar Habasha a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, ya shafe kwanaki uku a kasar dake gabashin Afrika.
-Kasar Saudiyya: A ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, shugaba Buhari ya tafi kasar Saudiyya, domin halartar taron zuba hannun jari da kuma aikin Umarah. Shugaba Buhari ya dawo Najeriya tare da mukarrabansa a ranar Juma’a 29 ga watan Oktoba.
-Burtaniya karo na biyu: Bayan dawowarsa daga Umrah a kasar Saudiyya ranar Juma’a 29 ga watan Oktoba, Shugaba Buhari ya cilla zuwa Burtaniya a karo na biyu a 2021 ranar 31 ga watan Oktoba. Shugaban ya sauka a birnin Glasgow, Scotland ne don halartan taron COP26 na taron gangamin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi.
Buhari ya gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.
-Kasar Faransa: Bayan shafe kwanaki a Scotland, Buhari ya dira kasar Faransa ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba domin zumunci da halartar taron zaman lafiya a birnin Faris. Shugaba Buhari ya zauna na kwanaki kadan a kasar Faransa, inda ya fita daga kasar a ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba.
-Kasar Afrika ta kudu: Daga kasar Faransa Buhari ya garzaya kasar Afrika ta kudu don halartan kasuwar bajakolin Afrika da aka yi a birnin Durban. Shugaban ya bar Faransa ne a ranar 13 ga watan Nuwamba tare da tawagarsa inda ya zarce birnin Durban na Afrika ta kudu. Kana shugaban ya dawo Najeriya a ranar 16 ga watan Nuwamba bayan shafe kwanaki akalla 16 a kasashe uku na waje.
-Daular larabawa, Dubai: Shugaba Buhari ya dira birnin Dubai, haddadiyar daular Larabawa da daren Laraba 1 ga watan Disamba domin halartan taron baja kolin EXPO 2020. Wannan taron baja koli ya auku ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamban 2021. Bayan shafe kwanaki a Dubai, Buhari ya dira filin jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja da yammacin Lahadi, 5 ga watan Disamba, 2021.
-Kasar Turkiyya: Jim kadan bayan dawowarsa daga daular larabawa, Shugaba Buhari ya sake cillawa zuwa kasar Turkiyya domin halartar wani taron. Jirgin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da Hajiya Aisha, ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja zuwa birnin Istanbul, Kasar Turkiyya a ranar Alhamis 16 ga watan Disamba.