Sababbin alkaluman da kamfanin NNPC ya fitar ya nuna cewa gwamnati ta fitar da Naira biliyan biyar domin cike gibin da aka samu a watan Yunin shekarar nan.
Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa NNPC ta biya makudan kudi a sakamakon banbamcin da aka samu wajen saida man fetur a gidajen mai ta yadda za a ci riba.
Abin da gwamnatin tarayya ta biya ta hannun NNPC shi ne Naira biliyan 5.348bn, ta hakane masu harkar mai za su ci riba a kan yadda su ka rika saida lita.
A cikin watan Maris, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da biyan tallafin man fetur. Wannan ya sa litar man fetur ya kara tsada a Najeriya.
An shafe kusan watanni uku ma’aikatar PPPRA ta na saida kudin man fetur ne a kowane wata tare da la’akari da yadda farashin gangar mai ya ke a kasuwar Duniya.
Bayanan da NNPC ta fitar na watan Yunin 2020, ya nuna an cirewa ‘yan kasuwa asara da biyansu Naira biliyan 5.348 da aka yi a wannan lokaci inji jaridar kasar.
NNPC ne ya ke shigo da mafi yawan tataccen man fetur a Najeriya. A watan Maris, rahotanni sun nuna kamfanin gwamnatin tarayyar ne kadai ya rika jigilar mai.
A watannin Afrilu da Mayu na shekarar nan, farashin da gwamnati ta tsaida wajen saida litar mai ya yi daidai da kudin da aka kashe wajen jigila da tace danyen man.
Zuwa watan Yuni, farashin litar mai ya zama ba zai iya maida kudin da aka kashe ba, wannan ya sa aka ware Naira biliyan biyar da nufin kawar da samun asara.
Wani babban jami’in NNPC, Kennie Obateru, ya bayyana cewa sun biya wannan kudi a Yuni ne saboda kayan da ke hannun ‘yan kasuwa bayan an cire talllafin man fetur.