Buhari Ya Cika Dukkanin Alkawurran Da Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya – Jigon APC

Babban Jigon jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Benuwai, Terhemba Ishegh, yace shugaba Buhari ya cika mafi yawan alƙawurran da ya ɗauka yayin yakin neman zaɓensa ga yan Najeriya, kuma ya kamata ‘yan Najeriya su nuna godiyarsu bisa ga hakan.

Mr. Ishegh, wanda tsohon sakataren dindindin ne a jihar Benuwai, ya faɗi hakane yayin wata hira da yayi da Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a makurɗi.

Yace Buhari ya kafa ayyuka da dama duk da ƙalubalen tsaron da ƙasar nan ke fama da shi, amma duk da haka gwamnatinsa ba ta yi ƙasa a guiwa ba har sai da ta cimma nasarori da dama.

A cewarsa, gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama a ɓangaren kayayyakin gwamnati, ilimi, tattalin arziki da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa. Buhari ya kafa tarihi Ishegh ya ƙara da cewa duk da halin kakanikayi da kasar nan ta faɗa, gwamnatin Buhari tayi kokari wajen aiwatar da manyan ayyuka a faɗin Najeriya.

“Buhari ya yi namijin kokari a mafi yawan yankuna, wasu yankunan ya fara zuba musu ayyuka amma sai wasu matsaloli su hana karisawa.” “A jimulla zan iya cewa shugaba Buhari ya kafa tarihin da babu wani shugaban Najeriya da ya taba yi a cikin shekaru shida.”

“A halin yanzu, duk da ƙalubalen tsaron da ake fama da shi kala daban-daban a yankunan Arewa-yamma, arewa-gabas, da arewa ta tsakiya sannan ya matsa zuwa kudu-yamma kudu-gabas.” “Amma gwamnati bata yi ƙasa a guiwa ba ta cigaba da yin iyakar kokarinta wajen kawo karshen matsalar a waɗannan yankuna,” inji shi.

Mr. Ishegh, yace idan ma aka cire shirye-shiryen da gwamnati ta kirkiro na walwala da jin daɗi ga talakawan Najeriya, Buhari ya samu damar aiwatar da muhimman ayyuka a kowane sashin ƙasar nan.

Ya bayyana irin waɗannan muhimman ayyuka da suka hada da hanyoyi, gada, makarantu da kuma garambawul ga ɓangaren samar da hasken wutar lantarki domin haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply