Buhari Ya Cika Dukkanin Alƙawurran Da Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya – Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawuran da ya yiwa ‘yan Najeriya lokacin da yake yakin neman zabe a 2015.

Gwamna ya bayyana hakan a jawabin Sallan da yayi ranar Juma’a a Birnin Kebbi, inda yace lamarin tsaro ya fi kyau yanzu fiye da lokacin da ya hau ragamar mulki.

Kan lamarin yaki da rashawa kuwa, ya ce Najeriya ta samu nasara wajen dakile masu cin hanci da rashawa. Bagudu ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan irin amincewar da yake da dan jihar Kebbi, wanda yake ministan shari’a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami.

Yace: “A kan lamarin tsaro, jami’an tsaro na iyakan kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana.” “A yanzu, babu yankin kasar nan dake karkashin yan ta’adda kamar yadda yake a baya.”

“Buhari ya samu nasaran inganta tattalin arzikin kasa, kamar yadda yayi alkawari.” “Buhari ya samu nasarar cika dukkan alkawura uku da yayi lokacin da yake yakin neman zabe a 2015.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply