Buhari Ya Cika Duk Al?awuran Da Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya – Sirika

Ministan Harkokin Jiragen Sama, Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa a duk fadin kasar nan da ta fito karara kudurce-kudurcen tallafawa talakkawa da kuma Darajja su kamar jam’iyyar shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Hadi Sirika ya bayyana haka ne jim kadan bayan sabunta katin rijistar sa a mazabatai ta Sirika B, da ke garin Shargalle a karamar Dutsi ta jihar Katsina da marecen jiya Lahadi.

Ministan ya ci gaba da cewa jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi rawar gani, musamman ta fuskar kawo gagarumin ci gaba ta fannoni daban-daban da kuma tallafawa talakkawa. An dauki shekara da shekaru ana yin mulki a kasar nan, Wanda da yawa al’ummar kasar nan ba su na’am da shi ba, amma jam’iyyar APC salonta shi ne kula da masu karamin karfi da Walwalar mutumin da ke kasa. Abun alfahari anan shi ne ana aiwatar da wadannan kyawawan manufofin na mu, tana fadi tana cikawa. Muna da manya-manyan mutane a cikinta,masu daraja da mutunci wadanda su nuna ‘yaya ne na halak kuma ba su ba da kunya ba, sun kahu akan gaskiya da adalci. Babba daga cikinmu shi ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, shi ke haskaka wannan jam’iyyar ta mu kuma a kullum yana kara mata farin jini da kwarjini.

Hadi Sirika, wanda na hannun damar Shugaban Kasa Buhari ya kara da cewa a bisa ga ayyukan alheri da jam’iyyar mu ta APC ke yi talakkawa na yabo kuma koda yaushe suna jinjina masa. Daga cikin abubuwan da mu ka yi alkawarin yin kafin a zabe mu a 2015, an samu biyan bukata ko ace mun cika su, saura kadan da suka rage suna nan tafe kan hanya da yardar Allah. Jam’iyyar APC ita tafi dai dai da dabi’un mu da Al’adun mu. Lokacin wadancan na mulki ba ka isa ka yi layi anan ba, ko rijistar katin jam’iyyar ko na zabe ba, kuma a wanye lafiya ba fargabar rashin tsaro ba. Amma zuwan jam’iyyar APC ta sauya wannan launin, an dora jama’a bisa turba mai kyau ta hanyar Inganta Tsaro, wanda kusan kowa shaida ne.

Da ya juya kan maganar rijista da sabunta katin jam’iyyar APC, Ministan ya ce mun zo ne domin mu jaddada yayanta ne halak malak. Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta hada ka a baya, wadda aka yi tsakanin jam’iyyu guda ukku, tun daga wancan lokacin zuwa yanzu, sai kara dankon zumunci mu ke, mun zama tsintsiya madauri daya. Maanar wannan sabunta katin rijistar, domin tabbacin ba mu tuna abinda ya wuce a baya can na maganar hada ka, muna maganar APC sak. Jam’iyyar Shugaban mu, Muhammadu Buhari. Mutane da yawa suna cewa kuri’un da aka kada mana a 2015, ba kuri’u ba ne tabatattu, aringizo aka yi har ma wasu na ba da labarai da misalai na karya akan haka. To wannan rijista da ake yi, ita ce za ta tabbatar da yawan al’ummar da ke tare da shugabanmu, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da wannan jam’iyyar mai albarka. Mutane duban suna jira a kawo masu domin su yi Rijistar, saboda wadda aka kawo a kowacce rumfa guda dari dari duk sun kare, saboda farin jinin da jamiyyar ke kara yi a tsakanin yan Nijeriya.

Daga karshe ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su fito kwansu da kwarkwatar su zuwa mazabu domin sabunta rijistar jam’iyyar APC mai albarka, domin nuna kuna tare da akida da sunnonin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Domin ci gaban kasar mu da yankin da mu ka fito, wadanda ba su samu halin yi ba a yanzu su kara hakuri kayan aikin na nan tafe, kowa muna son ya yi rijista, saboda ba mu kyamar kowa.

Related posts

Leave a Comment