Buhari Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro A Dukkanin Iyakokin Kasa

Sakamakon halin da harkar tsaro ke ?ara shiga a kasar nan musanman yankin Arewacin kasar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin gaggawa ya umarci hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da ta kara zage damtse wurin saka ido a iyakokin tudu na kasar nan saboda hauhawar rashin tsaron da ya addabi kasar nan.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Femi Adesina, mai ba shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai ya fitar, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, ya ce Buhari ya bada wannan umarnin ne a wani taro na yanar gizo da yayi a hukumar a Abuja.

Shugaban kasar yace, dole ne dukkan hukumomin tsaro su dage wurin kula da rayuka da kadarorin jama’a domin inganta tsaron kasar nan.

“Abin farin ciki ne ganin yadda muka kara gaba a matakin tsaro na duniya kuma ina amfani da wannan damar wurin kira ga dukkan hukumomin tsaro da su zage damtse.

“Ina tabbatar mana da cewa wannan mulkin zai bada dukkan goyon bayan da ake bukata domin ayyukanku.” Shugaban kasan yayi kira ga NIS da ta hada kai da hukumomin tsaro na fadin duniya kamar INTERPOL domin tsare iyakokin kasar nan.

“A matsayinku na hukumomin tsaro, ina kira gareku da ku dage wurin sauke nauyinku na ba iyakokinmu kariya yayin da kuke tabbatar da cewa duk wani mai laifi bai samu sassauci a kasar nan ba.”

Related posts

Leave a Comment