Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kara jibge jami’an tsaro a jiharsa, biyo bayan kashe wasu mutane 20 da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Talatar Mafara.
Matawalle ya fadi haka ne a ranar Juma’a, lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridar fadar shugaban kasa, bayan ganawarsa da shugaba Buhari.
Gwamnan ya bayyana cewa kimanin mutum 30 ne masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da suka fito daga kasashen China, Burkina Faso da Mali, aka mayar kasashensu.
Da yake magana kan dalilin ziyarar tasa, Matawalle, ya ce ya zo ne don yi wa shugaba Buharin jawabi kan halin tsaron da ake ciki a jihar zamfara.
Gwamnan Matawalle ya ce ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar na karuwa saboda rashin tsaro a iyakar da jihar take da su da Sokoto, Katsina da Nijar, ya yi fatan cewa matakan da hukumar kula da shige da fice ta kasa ta dauka zai taimaka wajen magance matsalar.
A wani labarin kuma wasu matasa fiye da 40 sunyi yunkurin balle runbun abincin Gwamnatin tarayya kamar yadda akayi a jihar legas ranar laraba. Saidai a wannan karon matasan ba suyi nasara ba sakamakon jami’an tsaro sun tarwatsa su a daidai lokacin.