Buhari Ya Bada Umarnin Garambawul Ga Shugabancin Tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin yin garambawul a dukkanin bangarorin tsaro na kasar. Mai bashi shawara kan tsaro na kasa Babagana Monguno ya bayyana hakan bayan fitowa daga taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya ce bayan tattauna batutuwan da suka shafi tsaron kasar a wajen taron, an kuma tattauna batu kan safara da tu’ammali da miyagun kwayoyi. A cewarsa, Nijeriya ta tashi daga cibiyar hada hada, zuwa cibiyar sarrafa magungunan da ake safararsu, wanda babbar matsala ce.

Ya yi nuni da cewa a kwanakin baya an rufe gine ginen sarrafa magunguna guda 17 a fadin kasar tare da yin kira da a hada hannu wajen kawo karshen fatauci da shan miyagun kwayoyi.

Har ila yau a wajen taron, shugabannin rundunonin tsaro sun yiwa Buhari bayani kan hanyoyin da suke ganin ya kamata abi don kawo karshen ta’addanci a kasar.

Mai ba shugaban kasar shawara ya kuma yi tsokaci kan harin da aka kaiwa gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da tawagarsa.

Monguno, ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa gwamna Zulum zai halarci taron ta yanar gizo kuma yayi bayani kan yadda lamarin ya faru.

A dangane da kashe kashe a Kudancin Kaduna, Monguno ya ce siyace kawai, kuma gwamnan jihar na yin iya bakin kokarinsa don kawo karshen lamarin.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha. Sauran sun hada da Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), shugabannin tsaro bisa jagorancin shugaban rundunar tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin.

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, da na sojin ruwa, V.A Ibok Ekwe Ibas, da na sojin sama, A.M Sadique Abubakar.

Daga cikin mahalarta taron akwai Sifeta Janar na ‘yan sanda, IGP Mohammed Adamu, shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Bichi, shugaban hukumar tsaro ta NIA, Ahmed Rufai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply