Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaron kasar nan su fantsama cikin dazukan kasar na su ceto duk wadanda ke tsare a hannun ?an bindiga.
Hakan ya biyo bayan ganawar gaggawa da shugaba Buhari yayi da manyan hafsoshin tsaron kasa Najeriya da kuma shugabannin hukumomin tsaron kasar ranar Alhamis a Abuja.
Mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaron kasa Babagana Monguno ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan an kammala ganawar.
Moguno ya ce ” Shugaba Buhari ya umarce dakarun kasar nan su fantsama dazukan kasar nan su ceto duk wani da ke tsare hannun ?an bindiga cikin gaggawa. Sannan kuma ya ce a tabbata an ceto su ba tare da an ji wa kowa rauni ba.
” Shugaba Buhari ta ce lokaci yayi da za akawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan sannan wadanda aka yi garkuwa da, ba na jirgin kasan Kaduna ba har da na ko ina dake hannun ?an bindiga duk a shiga daji a ceto su kaf din su.
A karshe Monguno ya yi kira ga ?an Najeriya, a hada kai da hukumomin tsaro domi ganin an kawa karshen wannan matsalar cikin gaggawa.
” Dole sai an ha?a karfi da karfe wajen kawo karshen wannan bala’i da ake fama da shi gaba ?ayan mu. Ba abu ne kawai na jami’an tsaro ba abu ne na mu duka.