Buhari Ya Bada Umarnin Ɗaukar Masu NCE Aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki daliban NCE aikin gwamnati kai tsaye da zaran sun kammala karatun su.

Ministan ilimi, Adamu Adamu a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba ya bayyana hakan, a babban birnin tarayya Abuja, yayin bukin murnar zagayowar ranar malamai ta duniya.

Haka zalika, shugaban kasar ya amince da bayar da gurbin karatu na kai tsaye tare da daukar nauyin karatun ‘ya’yan malamai.

Shugaban kasar, ya kuma bayar da umarni da a kara kudin albashin malaman makarantar tare da tsawaita shekarun aikin su.

Buhari ya kuma amince da karin albashi ga malaman makaranta, ya sanar da hakan a murnar ranar malamai ta duniya. Shugaban kasar ya kara wa’adin shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40, yayin da ya ke albishir da kara albashin malaman don basu kwarin guiwar gudanar da ayyukansu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply