Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Ya Amince Da Bada Tallafi Jihohin Da Aka Yi Ambaliya

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamiti na musamman da rarraba kayan tallafi ga jahohi 12 wanda ambaliyar ta lahanta a fadin kasar nan.

Shugaban ya dauki matakin ne biyo bayan karban bayanin ambaliyar ruwan daya faru a shekarar da muke bankwana da ita.

Kakakin Shugaban Garba Shehu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da akayi wa taken ‘bayanan ambaliyar ruwa’, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma ce za a sake tura tallafi ga jahohin da ambaliyar ta shafa. “Shugaba Buhari ya karbi rahoton a ranar Asabar kuma ya bada umarnin a kafa kwamiti na musamman don miki tallafin gaggawa ga jihohi 12 da abin ya shafa.

“Jihohin da za su karbi bakuncin kwamitin da za su raba tallafin ta hannun Hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) sun hada da:
Kebbi, Niger, Kwara, Kogi, Edo, Anambra, Delta, Kano, Jigawa, Rivers, Bayelsa da Adamawa.

“Daga cikin jihohin da kashin farko na tallafin shugaban kasar ya riska akwai; Kebbi, Niger, Kwara, Sokoto, Jigawa da kuma Kaduna. “Shugaba Buharin ya kuma bayyana alhininsa ga wadanda hadarin ta afkawa, wanda wasu sun rasa iyalansu, gidajensu da kuma muhimman abubuwa na bangaren noma da kiwonsu

“Shugaban kasar ya kuma bayyana bukatar sa ta haɗa kai tsakanin hukumomin gwamnatin jiha da na tarayya don kawo karshen ambaliyar, da kuma bukatar dogon nazari da kiyaye faruwar wannan iftila’i dama makamantansu.”

Exit mobile version