Buhari Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Malaman Makaranta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da biyan albashi na musamman ga malamai. Shugaban kasar ya kuma kara wa’adin shekarun aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba. Ya bayar da sanarwar ne a cikin wani jawabi na musamman da ya karanto yayinda yake wakiltan shugaban kasar a wajen taron zagayowar ranar malamai ta duniya.

A wani labarin kuma, Sunday Dare, ministan matasa da bunkasa wasanni, ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin daukar matasa miliyan daya aiki.

Dare ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar makon da ya gabata, a yayin wani bukin baje kolin kasuwanci na fasahar matasa a babban birnin tarayya Abuja.

Ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni tare da hadin guiwar gidauniyar ‘I Choose Life’ suka shirya taron. An shirya taron ne domin bukin murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun ‘yanci, da kuma taya matasa murna kan nasarar da suka samu a kasuwanci, kirkira, aikin hannu da fasahar zamani.

Labarai Makamanta

Leave a Reply