Buhari Ne Ya Haifar Da Matsalar Tsaro A Arewa – Galadima

Jigo a jam’iyar adawa ta PDP kuma tsohan na hannun damar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa rashin iya mulki da halin ko-in-kularsa ne ya haifar da wannan Kashe-kashe a arewacin Nijeriya, ake kashe mutane kamar kiyashi.

Alhaji Buba Galadima ya bayyana haka ne a Katsina, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, a wata walima da kanen tsohan Shugaban kasa, Marigayi Malam Umaru Musa, Kanal Audu Musa Yar’adua ya shirya domin taya shi murnar nadin da Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya tabbatar masa ta Matawallen Katsina.

Buba Galadima ya kara da cewa ‘in yi abun kirki nan ba jiharsa ba ce, ni ban ga kamoi ba, hatta wannan aikin wutar ta hanyar iska, an kasa kammalawa duk da jiharsa ce, bututun iskan duk sun karkare. Babbar matsalar Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne rashi iya mulki, idan ya iya ake kashe mutanen jiharsa da na arewacin Nijeriya kamar kiyashi. Kuma yanzu a kasar nan wa ke jin dadi. Ga halin ko in kula da jiharsa da yankinsa ke ciki, da gani kowa bai Isa ba. Har ila yau, talakkan kasar nan bai san hakkinsa ba.

Da ya juya maganar bude boda da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin yi ya ce daman can mu ‘yan arewa aka zalunta, saboda zai iya rufewa yarbawa ko inyamurai? Wannan ta’addanci ya faro ne sakamakon rashin aiki ga matasa. Ko lokacin mulkin Ojikwu ai jamhuriyar Nijar sun taimaki Nijeriya ta fuskoki da dama.

Labarai Makamanta

Leave a Reply