Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Ne Ya Bada Umarnin Cire Osinbajo A Kwamitin Zaben Tinubu – APC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jam’iyyar APC mai mulki ta yi ?arin haske kan dalilin da ya sa ba a saka sunan mataimakin shugaban ?asar Farfesa Osinbajo ba cikin kwamitin ya?in neman za?e na Asiwaju Bola Tinubu.

A ranar Asabar ne dai aka fitar da sunayen mutum 422 wa?anda za su jagoranci ya?in neman za?en shugaban ?asa a ?ar?ashin Jam’iyyar APC.

?aramin Ministan ?wadago na Festus Keyamo wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin ya?in neman za?en ya tabbatar da cewa Buhari ne ya ce kada a kuskura a saka sunan Osinbajo da sakataren gwamnati Boss Mustapha saboda za su mayar da hankali ne kan gudanar da ayyukan gwamnati.

Mista Keyamo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar sakamakon ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sunayen da aka fitar.

Exit mobile version