Buhari Ne Ya Bada Umarnin Cire Osinbajo A Kwamitin Zaben Tinubu – APC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jam’iyyar APC mai mulki ta yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ba a saka sunan mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Osinbajo ba cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na Asiwaju Bola Tinubu.

A ranar Asabar ne dai aka fitar da sunayen mutum 422 waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago na Festus Keyamo wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ya tabbatar da cewa Buhari ne ya ce kada a kuskura a saka sunan Osinbajo da sakataren gwamnati Boss Mustapha saboda za su mayar da hankali ne kan gudanar da ayyukan gwamnati.

Mista Keyamo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar sakamakon ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sunayen da aka fitar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply