Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU a Najeriya ta ce ba za ta dakatar da yajin-aikin da ta ke yi ba, har sai ta ga abin da ya ture wa Buzu na?i tsakanin ta da gwamnatin tarayya.
ASUU ta ce za ta cigaba da yajin-aikinta har sai gwamnatin tarayya ta saurari kokenta da kyau. Malaman jami’ar sun zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da hana su albashinsu domin ayi masu hora da yunwa saboda sun ki na’am da IPPIS.
Da ya ke magana da ‘yan jarida jim kadan bayan taron kungiyar a Jami’ar Neja-Delta, jihar Bayelsa, shugaban ASUU na yankin ya bayyana wannan.
Farfesa Uzo Onyebiama ya yi kira ga matasa da iyayen yara su ba su goyon-baya a fafatukar da su ke yi, a cewarsa domin ganin an gyara jami’o’in kasar.
Sauran wadanda su ka halarci taron manema labaran sun hada da shugaban ASUU na Jami’ar Otouke, Austen Sado da Dr. Kingdom Tonbara na UNIPORT.
“IPPIS ta zama makamin datse karfin ikon jami’o’i daga hannun shugabanninta, ta karbe masu karfin da aka ba su bayan sun yi fafatuka.” Inji Onyebiama.
Kungiyar ta ce: “Za mu cigaba da wannan fafatuka, sai an saurari kukanmu daidai gwargwado.”
A kwanakin baya kun ji cewa kungiyar ASUU ta fadi abin da zai hana Malaman jami’a koma wa aiki har yau, kungiyar ta ce ta na kokarin a koma karatu.
ASUU ta ce za ta iya koma wa bakin aiki da zarar gwamnati ta biya su duk wasu hakkokinsu.