Shugaban kasa Muhammadu Buhari na wata ganawa da wasu tsoffin shugabannin kasar Nijeriya a Fadar Shugaban ?asa Aso Rock Abuja.
Duk da cewa ba a fitar da hakikaninn abun da shugabannin ke tattauna wa ba,amman ana ganin bai rasa nasaba da halin matsalar tsaron da kasar ke ciki na zanga zangar End SARS.
Taron dai na gudana ne a fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari yayinda sauran tsaffin shugabannin ke halartar tattaunawar ta hanyar tangaraho.
Daga cikin masu halartar taron akwai Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Janar Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan da kuma Chief Ernest Shonekan.
Haka ma, mataimakinn shugaban kasa Yemi Osinbajo, mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, Babban Hafsan tsaro Janar Gabriel Olanisakin, Babban Sufeton ‘Yan Sanda Mohammad Adamu, Babban Daraktan hukumar tsaron farin kaya Yusuf Bichi da kuma Shugaban hukumar leken Asiri Ahmad Rufa’i duk suna halartar taron tare da shugaba Buhari.