Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisa ta takwas, Dino Melaye ya ce Najeriya kamar mota ce da bugaggen direba ke tukawa a ƙarƙashin mulkin APC bisa ga jagorancin Buhari.
Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Dino Melaye, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP ya yi gargadin cewa, babu wani bangare a Najeriya da ke zaune lafiya.
Da yake siffanta tafiyar dan takarar shugaban kasan PDP a zaben 2023, ya ce Atiku babu abin da ya sa a gaba kamar kawo mafita ga matsalolin Najeriya. “Atiku kwararren mai iya warware matsaloli ne. Abin da nake fadi shine, yana da gogewa da kwarewa wajen warware matsaloli saboda yakan fahimci matsalolin. “Ya san kasar ciki da waje, kasancewarsa mataimakin shugaban kasa kuma fitacce a hakan.”