Lauyan tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta’annati, EFCC Ibrahim Magu, Barista Tosin Ojaomo a ranar Talata ya koka kan cewa ba a yi adalci ba a game da mataki da sakayar da aka yi wa Ibrahim Magu.
Lauya Ojaomo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Politics Today’ na gidan Talabijin na Channels.
An kaddamar da kwamitin Ayo-Salami ne domin yin bincike game da dakataccen shugaban rikon kwaryan na hukumar yaki da rashawar a shekarar data gabata.
“kwatsam, rahoto bai fito ba, sai aka yi wani nadin … ana iya gani karara cewa ba a yi wa Magu adalci ba a wannan batun, muna magana kan mutuncin da kimar mutane ne a nan.
“Ba Magu kadai abin ya shafa ba, akwai wasu mutane a hukumar da aka dakatar da su, dukkan mutanen nan, suna iya rasa kimarsu kamar an manta da batunsu ne.
“Idan ana batun adalci, na kan tuna da kalaman Mai shari’a Oputa, wanda ya yi magana kan adalci, ya ce akwai abubuwa 3 a batun adalci: adalci ga wanda ya yi kara, adalci ga wanda ake zargi da adalci ga al’umma.
“A wannan batun, ba a yi wa ‘yan Nigeria adalci ba domin kowa na sa ran sanin sakamakon binciken.
Akwai labarai da yawa game da Magu a kafafen watsa labarai, yanzu an bar mutane cikin waswasi.”