Buhari Bai Da Hannu A Halin Da Najeriya Ta Tsinci Kanta – Malamin Addini

Babban Malamin addinin Kirista mazaunin Birtaniya kuma babban fasto a cocin Faith Tabernacle, Apostle Alfred Williams, ya ce kada a dora wa Buhari laifi bisa matsalolin Najeriya Williams ya ce tsarin yadda Najeriya ta ke ne ke kawo cikas ga kyawawan niyya da Buhari ke da shi na ciyar da ƙasa gaba.

Ya yi magana yayin ziyara da ya kai gidan talabijin na kasa, NTA, a Abeokuta, Jihar Ogun. Malamin addinin ya ce tsarin Najeriya ba zai bari kowa ya iya tabbuka komai ba a kasar.

“Ba Buhari bane matsalar Najeriya. Matsalar tsarin yadda kasar ta ke ne. Idan kai ko ni, fasto ko fasto Adeboye na Redeemed (RCCG), wanda duk muke girmamawa, ko Fasto Kumuyi ya zama shugaban kasa, za su shiga damuwa. “Don haka, ba mutumin da ke kujerar bane, tsarin kasar ce ke hana mutum aiwatar da niyyarsa ta alheri.

Idan muka mayar da hankali kan Buhari, idan wani ya hau kujerar kuma tsarin bai canja ba, zai gaza kamar yadda Buhari ya gaza.” Williams ya ce Najeriya na bukatar shugaban da zai yi wa al’umma hidima a yayin da kasar ke shirin babban zaben shekarar 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply