Buhari Abin Koyi Ne A Siyasar Afirka – Gwamnatin Amurka

Shugaban kasa Amurka Joe Biden ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa shayar da ‘yan Najeriya romon dimokradiyya da fadada dimokradiyar a nahiyar Afrika.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu bayan ganawar Buhari da Biden a birnin Washington ranar Laraba.

Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Amurka don halartar wani taron shugabannnin kasashen Afrika a makon da ya gabata.

Shugaban na Amurka ya ce, wannan taro Amurka ta hada shi domin tattaunawa da shugabannin Afrika kan lamurran da suka shafi alakarsu da kasar gabanin zaben da kasar za ta gudanar nan ba da dadewa ba.

Biden ya ce ya bibiyi tafarkin Buhari tun yana shugaban adawa har yazo ya zama shugaban kasa a Najeriya, ya gamsu da nagartarsa. Ya kuma kara da cewa, abin a yaba ne yadda Najeriya ta zama abin kwatance a nahiyar Afrika wajen fadada tafarkin dimokradiyya.

Hakazalika, ya yabawa shugaban bisa ba hukumar zabe mai zaman kanta INEC damar yin ayyukanta yadda ya dace ba tare da wata tsangwama ba.

Da yake martani, shugaba Buhari ya bayyana godiya da yadda shugaban na Amurka ya yabe shi, kana ya yi masa fatan nasara a zaben da za a gudanar nan gaba a Amurka. Ya kuma gode masa bisa shirya wannan babban taro mai tarihi da tasiri ga shugabannin na Afrika.

Labarai Makamanta

Leave a Reply