Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gana da jihohi ranar Talata don tattaunawa kan hanyoyin sake bude makarantun firamare da sakandire.
A yanzu haka dai Makarantu fadin kasar suna nan a kulle, tun cikin watan Maris sakamakon barkewar cutar corona virus a cikin kasar wanda ya haifar da ‘yan Najeriya sama da mutum 25,000, sun harbu da cutar.
Shugaban kwamitin yaki da cutar corona virus, Boss Mustapha, a ranar Litinin ya ba da sanarwar sake bude makarantun, yana mai cewa hakan zai ba da damar baiwa daliban da ke karatun digiri su ci gaba da shirye-shiryen jarabawar su.
Duk da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sake bu?e makarantu, har yanzu dai ana ta duba yuwuwar hakan a yayin da gwamnatocin jihohi ke gwagwarmayar yanke hukunci kan ranakun sake bu?e makarantu.
Kwamishinan Ilimi a jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru, ya ce gwamnatin jihar na kokari wajan duba yuwuwar bude makarantu don gaggauta dawo da dalibai a cikin azuzuwan su, Amma bai bayar da takamaiman ranar sake bu?ewa ba.
Haka itama Kwamishinan Ilimi ta jihar Kwara Fatimah Ahmed, ta ce babu wani umarni tukunna game da lokacin da ?aliban zasu koma.
Sai dai kungiyar likitoci da kungiyar malamai basu goyi bayan hakan ba, inda suka soki lamirin sake yiwuwar bude makarantu a wanann lokaci. Inda suka bayyana cewa hakan tamkar baraza nane ga lafiyar malamai da kuma Dalubai.