Buɗe Boda Ne Mafita Akan Tsadar Shinkafa – Rimingado

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano, tace ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta magance ta’azzarar farashin shinkafa, sai da a wannan karon abin ya ci tura.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimingado ya ce ba zasu iya daidaita farashin shinkafa ba a yanzu domin matsalar ba daga masu samar da shinkafar ba ne.

“Hana shigo da shinkafar da gwamnatin tarayya tayi shine musabbabin da ya haifar da tsadar shinkafar, kuma gwamnatocin jihohi ba zasu iya taɓuka komai a kai ba.

“Gwamnatin tarayya ce kaɗai za ta iya kawo ƙarshen matsalar ta hanyar bada dama a cigaba da shigo da shinkafar kamar yadda ake shigowa da alkama”. Inji shi

Rimingado ya bayyana hakan, ta cikin shirin Inda Ranka na gidan radiyo Freedom.

Labarai Makamanta

Leave a Reply