Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa wani sansanin ‘?an gudun hijira dake Maiduguri shigar ba-zata inda ya gano ?aruruwan ‘?an gudun hijirar na bogi dan?are cikin sansanin.
Sanarwar da gwamnatin Jihar Borno ta aike wa ?ungiyar ‘yan Jaridu ta ce daga cikin ‘?an gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji, 650 daga cikinsu na bogi ne.
Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS dake birnin Maiduguri inda ake kula da mutanen ?aramar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya raba da gidajensu.
“Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin ‘?an gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ‘?an gudun hijirar,” in ji sanarwar.
Sannan ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin gano masu ?aryar cewa ‘?an gudun hijira ne da ke shafe kwanaki a sansanin suna kar?ar abincin da aka tanadar wa ‘?an gudun hijira, kuma idan dare ya yi su tafi gidajensu.
Jama’a na cigaba da yabawa gami da jinjina ga gwamnan bisa namijin ?o?arin da yake wajen inganta al’amura da rayuwar jama’ar Jihar gaba daya.