Gwamnatin jihar Borno ta samar da filayen noma dubu goma a kananan hukumomin Bama da Konduga.
Kwamishinan ma’aikatar ayyukan noma Engr Bukar Talba ne ya bayyana hakan, ya yin da ya ziyarci filayen noma da gwamantin jihar ta samar wanda kowane ya kai tsawon kilomita sha bakwai domin gudanar da ayyukan noma.
Bukar Talba yace farfado da ayyukan noma na daga cikin manufofin gwamnatin Babagana Umara Zulum domin raya kasa.
Idan za a iya tunawa dai, gwamatin jihar Borno ta ce tana kokarin samar da filayen noma a sassan jihar domin rage radadin kangin rayuwa da kuma samar da abinci da kuma yaki da talauci.
Daga Adamu Aliyu Ngulde Maiduguri