Borno: Zulum Ya Rabawa ?ananan ‘Yan Kasuwa Jarin Miliyan 32

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a yau Lahadi ya raba tsabar kudi naira miliyan 32 ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa 704 a birnin Maiduguri, cikin ‘kasa da mako guda gwamnan ya raba akalla naira miliyan 154 ga kananan ‘yan kasuwa don bunkasa harkokin tattalin arzikin da kuma yaki talauci.

An kaddamanar da bada jarin ne akan hanyar Damboa inda mutane 304 masu matsakaitan sana’o’i suka samu Naira 50,000 kowannen su, a anguwar Kulo Gumna, wasu 400 sun amfana da Naira 50,000 kowannen su duka a birnin Maiduguri.

Kafin haka, an raba Naira miliyan 75 a baya ga masu sana’ar sai da goro, naira miliyan 20 ga ’yan kasuwa a kusa da Dandal, da kuma wasu naira miliyan 24 ga’ yan kasuwar da ke shataletalen kasuwar kwastan a birnin Maiduguri. Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun sami naira 50,000 kowanne su don ha?aka kasuwancin su.

A wajen rabiyar jarin na yau Lahadi, Gwamna Zulum ya kalubalanci wadanda suka amfana da tallafin su yi amfani da shi don karfafa kasuwancin su, rabon jarin yana ‘daya daga cikin al’kawuran da Gwamnan yayi lokacin yakin neman zabe ga matsakaitan yan kasuwa.

Da yake zantawa da manema labarai, Gwamna Zulum ya ce: “Muna son mu karfafa musu guiwa ne akan kasuwan cin su, kuna sane da cewar da yawa daga cikin mutanen mu sun rasa harkokin na yau da kullum wanda suke dogaro da shi don gudanar da rayuwar su sakamakon ayyaukan masu tayar da kayar baya. Samar da ayyuka na ‘daya daga cikin abubuwan da ke cikin tsarukan mu 10, don haka ne ma muke cika alkawuran da muka dauka lokacin yakin neman zabe don ganin al’ummar mu sun samu abin dogaro da kai. Ina kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da shi ta hanyar da aka tsara domin ya bunkasa ya kuma yi musu amfani a rayuwar su”.

Shugaban Bankin Borno Renaissance Microfinance Bank, Dakta Bello A. Ibrahim, wanda yake da alhakin raba kudin ga ‘yan kasuwa ya ce sama da Naira biliyan daya zuwa yanzu aka cikin ‘kasa da shekara guda ga kungiyoyi ‘yan kasuwa daban-daban.

Related posts

Leave a Comment