Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Majalisar dokokin jihar ta amince mataimakin gwamnan jihar Umar Usman Kadafur ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayun 2021.
Hakan na zuwa ne sakamakon hutu na kwanaki 21 da Gwamna Babagana Zulum zai tafi kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter.
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarin Lawan ne ya sanar da amincewar majalisar a wasika mai dauke da kwanan wata na 26 ga watan Afrilu. Zulum ya rubutu wasikar neman samun amincewar majalisar ne a ranar 23 ga watan Afrilun 2021 domin ya samu ya tafi hutun kwanaki 21.
Sashi na 190 (1) na kudin tsarin mulki ya bukaci gwamnan ya nemi izinin majalisar dokokin domin nada mataimakin gwamna ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya domin ya samu ikon gudanar da mulki a jihar ba tare da ya tuntubi gwamna ba.
Gwamnan ya umurci dukkan ma’aikatan gwamnati da hukumomi su bada cikaken hadin kai bisa mika mulkin da ya yi ga mataimakinsa,” a cewar kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau.