Borno: Zulum Ya Ginawa ‘Yan Gudun Hijira Gidaje

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta samar wa mutane 2,800 mahalli bayan rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu a yankin Ajiri na ?aramar Hukumar Mafa da ke jihar.

Wa?anda abin ya shafa dai sun bar gidajensu ne bayan hare-haren ?ungiyar Boko Haram da ke i?irarin jihadi sannan suka nemi mafaka a Maiduguri, babban birnin jihar cikin shekara biyar da suka wuce.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito kwamishinan ma’aikatar sake gina Borno ta Rehabilitation, Reconstruction and Resettlement (RRR) yana bayyana hakan yayin mi?a rukunin gidaje 500 ga mutanen a Mafa ranar Juma’a.

Mustapha Gubio ya ce mutanen wa?anda a da suke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Customs House Internally Displaced Persons, sun za?i su koma gidajensu da kansu domin ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

An fatattaki mutanen garin ne bayan wani hari, gwamnatin jiha ta hannun ma’aikatar RRR ta gina sabbin gida 500 tare da saka duk abubuwan da ake bu?ata domin ?arfafa musu gwiwar komawa gida,” in ji kwamishinan.

Related posts

Leave a Comment