Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Laraba ya kaddamar da shirin bayar da bashin N1bn ga kanana da matsakaitan yan kasuwa a jihar, domin tsayawa akan ƙafafuwan su.
Wakilinmu ya halarci taron kaddamar da shirin ya ruwaito cewa yawancin wadanda suka ci gajiyar bashin mata ne da gamayyar kungiyoyin yan kasuwa da suka tsaya musu jingina.
A cewar gwamnan, wannan shine shafin farko na rabon bashin milyan biyu ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da gwamnatin jihar tare da hadin kan bankin masana’antu ke shirin yi ta hannun bankin Borno Renaissance Micro Finance Bank .
Zulum ya sanar da cewa wadanda zasu ci gajiyar wannan bashi sune kananan ‘yan kasuwan da rikicin Boko Haram da annobar COVID-19 ta nakasa. Ya ce wannan shirin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin jihar, da samar da ayyukan yi, tare da fadada hanyoyin samun kudi ga matasa a jihar.
Yace: “A yau, mutane 15,861, ‘yan kungiyoyin yan kasuwa 12 zasu amfana da lamunin N994,930,000.00.” “Bashin bai bukatar kudin ruwa kuma mutum zai iya biya cikin shekaru 4 tare da damar jinkirin watanni 6 da ake kyautata zaton cewa abubuwa zasu gyaru kuma a samu riba,”
Ya yi kira ga wadanda suka amfana da bashin nan su sanya kudin cikin kasuwancinsu kuma kada suyi watanda. Hakazalika ya yi kira ga kungiyoyin su lura da mambobinsu kuma su tabbatar da cewa an biya bashin.
“Duk wanda ya samu nasarar biyan bashin cikin lokacin da aka kayyade, za’a yafe masa rabin kudin kuma zai cancanci kara amsan wani bashin.” Bugu da kari, gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa na cikin tattaunawa da babbar bankin tarayya CBN, bankin cigaban Afrika AfDB da bankin cigaban Musulinci IDB domin samar da wasu hanyoyin amfanar kanana da matsakaitan manoma a jihar.