Borno: Za Mu ?auki Sabbin Dabarun Ya?i Da Ta’addanci – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa zai dauki sabbin dubarun kariya game da yadda yake aiwatar da manufofin kawo zaman lafiya a fadin jihar Borno. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnan ya hadu da harin ‘yan kungiyar boko haram har sau biyu a garin mungonu.

Zulum ya bayar da wannan tabbacin ne ga mambobin majalisar dokokin tarayya na Borno, wanda suka kai masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai masa kwanan nan.

Mambobin majalisar dokokin karkashin jagorancin tsohon gwamnan Borno kuma sanata mai ci a yanzu, Kashim Stettima, sun nuna alhininsu ga gwamnan.

Akalla jami’an tsaro 15 da suka hada da sojoji, yan sanda da yan sa-kai na JTF ne suka rasa rayukansu a harin na makon da ya gabata, yayinda wasu takwas suka jikkata.

Sun kuma yi addu’a ga dukkanin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a yayin arangama da yan ta’addan.

Gwamna Zulum wanda ya nuna farin ciki da ziyararsu, ya bayyana cewa hakan alamun hadin kai da goyon baya ne a gare shi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai kuma ya bayyana cewa hakan ba zai sanyaya masa gwiwa ba a jajircewasa na dawo da zaman lafiya a jihar Borno nan da dan wani lokaci kadan.

Gwamnan ya ce har yanzu halin da jihar ke ciki na da matukar hatsari musamman ta fuskacin shi kansa da wadanda suka yi masa rakiya zuwa yankunan arewacin jihar Borno.

Zulum ya kara da cewa gwamnatinsa na burin dawo da zaman lafiya a gabar tekun Chadi, yankin Sambisa da tsaunukan Mandara, wanda ke samar da albarkatun gona ga manoman karkara a jihar.

Related posts

Leave a Comment