Gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanya yara 1,163 na mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a wata makaranta a garin da aka kwato daga hannun masu tayar da kayar baya a jihar ta Borno.
Gwamnan, wanda ya sanya ido a kan sanya yara ‘yan gudun hijirar a garin Damasak, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai yankin ranar Litinin, ya ce atisayen wani yunkuri ne na tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su shiga makarantu. Ya ce iyaye da masu rikon yara wadanda ke ba wa ‘ya’yansu damar zuwa makarantu ne za a yi la’akari da su game da kunshin walwala da jin dadin jama’a daga gwamnati.
Gwamna Zulum Ya ce manufar ita ce a karfafa wa iyaye gwiwa su ilimantar da ’ya’yansu. Ya tabbatar wa dukkan daliban makarantar sakandare a Damasak da wadanda suka rubuta jarabawar kammala sakandare na goyon bayan gwamnati.
Gwamna Zulum ya kasance a Damasak, mai tazarar kilomita 189 zuwa Maiduguri tun ranar Asabar don raba kayan abinci da sauran taimako ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Yawancin ‘yan gudun hijirar sun fito ne daga wata karamar hukumar da ke kusa.
Damasak, hedikwatar karamar hukumar Mobbar, ta taba kasancewa matattarar mayakan Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram ta lalata kimanin makarantu 1; 400 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kuma fiye da rabin makarantun na Borno sun kasance a rufe kusan shekaru goma yanzu saboda tashin hankali, in ji wani rahoto na shekara ta 2017 na UNICEF.
Kusan dukkan makarantun da ke arewacin Borno, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula, kungiyar Boko Haram ta kone yayin da wasu kalilan suka koma sansanonin soja.