A ranar Alhamis da yamma, rundunar Army Super Camp suka mayar da harin da ‘yan ta’adda suka kai Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno, inda suka yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram mummunan kisan kiyashi.
Tun da fari dai ‘yan Boko Haram ne suka kai harin, sun kai harin ne bayan kwanaki kadan da shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai yayi sintiri a dajin Ngamdu-Goniri a ranar 17 ga watan Oktoba. Ngamdu iyakar jihar Borno da jihar Yobe ne, kusa da dajin Alagarno.
Hukumar tsaro ta sanar da harin da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai Doksa, karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Al’amura sun fara cabewa ne tun bayan da sojoji suka fara kutsa kai da wani sabon shirin su na ‘Operation Fireball’ don kai hari ga ‘yan ta’addan da ke zagayen Timbuktu, tsakanin dajin Sambisa, tsaunikan Mandara da tafkin Chadi.
Miyagun ‘yan ta’addan sun dade suna addabar Arewa maso gabas a Najeriya, wanda hakan ya janyo mutuwar fiye da mutane 30,000 da kuma bata da rasa gidajen fiye da mutane Miliyan 2.
Sai dai wani harin da dakarun Sojin suka kai yayi matuƙar tasiri wajen ƙara karya laggon ‘yan ta’addan na Boko Haram, rahotanni sun bayyana cewar an karkashe ‘yan ta’addan masu yawa.