Borno: Mayakan Boko Haram Sun Kone Gidajen ‘Yan Gudun Hijira

IMG 20240229 WA0096

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kona sabbin gidajen da aka gina domin sake tsuganar da ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.

Mayakan sun kutsa kauyen Gajibo da ke karamar hukumar ne suna harbi kan mai uwa da wabi sannan suka cinna wa sabbin gidaje 25 wuta.

Yan Boko Haram Sun ce, matan da su ka sace a Ngala jihar Borno a ran Talata, Aikin kunun Azumi zasuyi mu su, sai bayan Salla zasu sakosu.

Wani ganau, Modu Kundiri, wanda ke hanyar zuwa Maiduguri daga Gomboru, ya ce sojoji sun dakatar da motocinsu na kusan awa wuku a kauyen Logomani kafin daga bisani su bude hanya.

“Na ga akalla 25 daga cikin sabbin gidajen suna ci da wuta a kauyen Gajibo da ke yankin Dikwa,”in ji Modu.

Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, wanda ya tabbatar da harin na safiyar ranar Talata da kuma kona gidajen, ya ce maharan sun dasa abubwa fashewa a wurin da ake aikin ginin gidajen.

“Sojoji sun shaida mana cewa maharan sun dasa ababen fashewa a wurin, amma sojojin sun gano wasu bama-baman,” a garin na Gajibo mai nisan kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply