Borno: Mayaƙan ISWAP Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawa

Mayakan jihadi masu alaka da kungiyar IS a yammacin Afrika sun yi garkuwa da daruruwan mutane a wani gari da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda rahotanni ke cewa.

‘Yan ta’addar na Kungiyar ISWAP sun mamaye garin Kukawa da ke yankin Tafkin Chadi tare da kama mutanen da suka koma gidajensu bayan sun shafe kusan shekaru biyu a sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda Babakura Kolo, wani shugaban ‘yan sa-kai ya bayyana.

‘Yan ta’addar da suka isa garin a cikin manyan motoci 22 sun kai farmakin ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar talata, yayin da suka yi artabu da sojojin da ke tsaren garin.

A ranar 2 ga watan Agustan da muke ciki ne mazauna Kukawa suka koma gidajensu karkashin rakiyar sojoji bayan gwamnatin jihar Borno ta bada umarni.

Mutanen sun samu mafaka ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri mai nisan kilomita 120 daga garin na Kukawa da suka tsere masa a cikin watan Nuwamban shekarar 2018 sakamakon hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wani shugaban al’ummar yankin ya ce, mutanen sun koma gidajensu ne da zummar gyara filayensu na noma, amma suka fada a hannun ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta

Leave a Reply