An ceto ma’aikatan gwamnatin jihar Borno 5 da ‘yan kungiyar ISWAP sukayi garkuwa dasu watan da ya gabata.
Anyi garkuwa da ma’aikatan RRR dinne, yayin da suke kan hanya tsakanin Maiduguri da Monguno. Ma’aikatan 5 sun bayyana a wani bidiyo ne jiya suna neman taimakon gwamnatin jihar Borno.
‘Yan ta’addan sun yi ikirarin kai wa ma’aikatan gwamnati farmaki akan abin da suka kira aikin da suke yi wa “makiya addinin musulinci.” ‘Yan ta’addan sun yi ikirarin hakan kafin su kai wa ma’aikatan farmaki, inda suka kama wasu ma’aikatan tsaro a watan Agusta.
“Da farko anyi tunanin ba ma’aikatan gwamnati bane,” kamar yadda labarin yazo. “Amma sai suka canja ra’ayinsu da suka gano cewa kananan ma’aikatan RRR suka kama, mafi yawa ma leburori ne,”.
Jaridar Premium Times tace da taimakon Umul-Kalthum Abdurrahman, shugabar wata gidauniya ta KFP aka samu suka sako ma’aikatan.
A wata hira da Premium Times tayi da Ummu-kalthum, ta tabbatar da cewa gwamnati da kuma ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa dasu ne suka tuntube ta, inda ta tsaya tsayin-daka domin ganin ta fitar da ma’aikatan ba tare da an basu ko sisi ba.
Tace, “Abinda na sani shine, gwamnati da ‘yan uwan wadanda aka kama sun tuntubemu sakamakon taimakon ceto mutane da dama da suka samu labarin munyi, daga hannun ‘yan ta’addan.
“Mun samu tattaunawa da ‘yan ta’addan ta wasu lambobi, inda suka ce zasu kashe su in dai bamu yi wani abu ba da wuri. Sai suka ce zasu bada kwanaki zasu yi rangwame na ‘yan kwanaki.”