Borno: Har Yanzu Boko Haram Ne Ke Rike Da Ƙananan Hukumomi Uku – Kakakin Majalisa

Babu dan Adam ko guda dake zaune a kananan hukumomin jihar Borno uku saboda matsalan rashin tsaro, kakakin majalisar dokokin jihar, AbdulKareem Lawan, ya bayyana ranar Alhamis.

Kananan hukumomin sune Guzamala, Marte da Abadam, dukkansu na arewacin jihar kuma sun fuskanci kalubale iri-iri sakamakon yakin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa tsawon shekaru 11 yanzu.

Kakakin ya ce a karamar hukumar Guzamala, mai hedkwata A Gudumbali, kuma mai nisan kilomita 125 da Maiduguri, babu Soja ko mai farin hula daya dake rayuwa a garin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin taraya ta kara yawan Sojojin domin kare Arewacin Borno saboda masu zama a sansanin gudun Hijra su koma muhallansu.

Lawan ya yi wannan jawabi ne yayinda yake karban bakuncin tawagar kungiyar matasan Guzamala karkashin jagorancin shugabansu, Babagana Alkali, a Maiduguri. Ya ce ya zama wajibi yayi magana saboda duniya ta san halin da ake ciki a Guzamala, Marte da Abadam.

Abin ya tayar min da hankali da safen nan da na saurari jawabin shugaban tawagar.” Yace “A matsayina na wakilinku, wajibi ne in bayyana muku abinda ake ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply