Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa tawagar gwamnan jihar Babagana Zulum ta yi hatsarin mota.
Lamarin ya faru ne dazun nan a yayin da gwamnan yake kan hanyar komawa Maiduguri daga garin Mafa, a cewar wasu mutane da ke cikin tawagar.
Sun shaida wa BBC cewa hatsarin ya faru ne sakamakon ficewar tayar wata mota da ke cikin tawagar kuma mutum uku sun mutu.
Cikin mutanen da suka mutu har da Mai Kanuribe na Lagos, Mai Mohammed Mustapha da abokinsa da kuma direbansa, a cewar ganau.
Sai dai rahotanni sun ce babu abin da ya sami Gwamna Zulum.
Bayanai sun nuna cewa gwamnan da tawagarsa sun je garin Mafa ne a ci gaba da aikin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya take yi na sabunta rijistar ‘ya’yanta.
A baya dai gwamnan na jihar Borno ya tsallake rijiya da baya sau biyu sakamakon harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wa tawagarsa.