Borno: Gobara Ta Ci Rayuka A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

IMG 20240313 WA0044

Lamarain, a cewar kakakin rundunar, ASP Nahum Daso Kenneth ya faru ne da safiyar yau da ƙarfe 10.

Ya bayyana cewa lamarin ya ritsa da yara ƙanana biyu – namiji da mace.

ASP Kenneth, ya ce ba a kai ga sanin musabbabin tashin wutar ba amma ana ci gaba da gudanar da bincike a kai.

Ya ƙara da cewa za su sanar da mutane abin da bincikensu ya gano game da tashin gobarar inda ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake cewa nakiya ce da ta tashi ta haddasa gobarar.

Jihar Borno dai na fama da rikicin masu ikirarin Jihadi fiye da shekara 10 ke nan lamarin da ya janyo asarar mutane da dama tare da ɗaiɗaita wasu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply