Borno Da Katsina Ya Kamata Ka Kai Ziyara Ba Kasar Mali Ba – PDP Ga Buhari

Jam’iyyar hammaya ta PDP ta cacaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan zuwa kasar Mali sasanci a yayin da kasarsa ke cikin matsala.

Sanarwar da PDP ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta bayyana cewa, a yayin da shugaban kasar ya fara bude kofarsa bayan dadewa bai fito daga fadar sa ba, abin mamaki sai ya tafi kasar Mali.

Tace Nijeriya na fama da matsalar tsaro da ta cin hanci da ta amfani da mukaman gwamnati ba daidai ba amma duk shugaban ya tsallake ya je sasancin da bai ma yi nasara ba.

PDP tace ina ma a ce Borno ko Katsina ko kuwa sansanin soji yaje dan ganin irin matsalolin da suke fuskanta? Tace bata adawa da maganin matsalar kasar Mali amma ta yaya gidanka na ci da wuta zaka je kana kokarin kashe na wani?

Labarai Makamanta

Leave a Reply