Kwamishinan shari’a na jihar Borno, Kaka Lawan, ya yi bayanin yadda mayakan Boko Haram suka kai wa gwamnan jihar, Babagana Zulum hari.
Lawan ya ce an fara kai wa gwamnan hari ne da abubuwan fashewa da aka dasa a hanyar da tawagarsa za su bi, sannan ya ce an kai hari na biyu ne ta hanyar daura wa jaki bam.
Yan ta’addan Boko haram sun kai wa Zulum wasu hare-hare mabanbanta har guda biyu cikin yan kwanakin da suka gabata.
Harin farko da yan ta’addan suka kai wa tawaagar motocin gwamnan a ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki harda jami’an soji, yan sanda da na CJTF.
Kasa da sa’o’i 48 bayan afkuwar lamarin, a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, an sake kai wa ayarin gwamnan hari a hanyarsa ta dawowa daga garin Baga.
A wata hira da sashin Hausa na BBC, Lawan, wanda ya kasance a cikin tawagar gwamnan a lokacin hare-haren biyu, ya ce yan ta’addan sun dana bama-bamai uku a lokacin da gwamnan ya doshi garin Baga daga Monguno a karamar hukumar Monguno.
“Muna a hanyarmu ta dawowa Monguno daga Baga lokacin da yan ta’addan suka dana bama-bamai a wurare uku mabanbanta. Dukkanin bama-baman sun tashi a lokaci guda,” in ji kwamishinan.
Ya kara da cewa: ”Daga nan sai mayakan suka bi mu da barin wuta. An kwashe fiye da mintuna 20 ana harbe-harbe kafin suka janye.”
Lawan ya ce mayakan sun yi musu kwanton-bauna ne yana mai cewa ana tsaka da harbe-harbe sai jami’an tsaro suka umarci motar da gwamnan ke ciki ka da ta yi gaba.
Ya ci gaba da cewa, a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida sai mayakan suka daura wa “jaki bam aka sa masa jarkoki irin na ruwa kamar wanda zai je diban ruwa.
“Su wadannan yan ta’adda suna boye a baya, to shi ne shi sojan da yake kan mota ya dauke jakin da harbi. Sai bam ya tashi, sannan yan ta’addan suka dunga harbi da bindiga.”
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa a tawagar gwamnan harda kwamishinoni hudu, sai dai ya ce babu abun da ya same su.
Ya yaba wa jam’ian tsaro bisa kariyar da suke bai wa al’ummar jihar Borno domin tabbatar da zaman lafiya.