‘Yan Bindiga da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne sun sake kai wa ayarin Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum hari a kokarinsa na shiga duba ’yan gudun hijira a garin Baga jiya asabar 21 ga watan nuwanba.
Majiyar jaridar muryar yanci ta shaida mana cewar nn kaiwa gwamnan harin ne a safiyar jiya asabar a dai-dai kauyen da ake kira Kwayamti da ke da nisan kilomita 60 daga Maiduguri. Sai dai kuma rashin sabis na salula a wurin ya hana fitar labarin har sai a daren Asabar wayewar garin Lahadin nan.
Ko a watannin baya bayan nan gwamnan ya tsalake rijiya da baya inda mayakan boko haram sukai yunkurin hallaka shi a hanyar sa ta zuwa baga.
A sakamakon harin dai sojoji bakwai sun rasa rayukansu, ya yin da dan sintiri na civilian JTF guda daya shi ma ya sadaukar da rayuwarsa.
Babu wani abu da ya samu Gwamna Zulum domin tun farko shi an dauke shi a jirgin sama zuwa Baga.
Wannan shi ne karo na hudu a cikin wannan shekarar da ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne ke kai wa ayarin gwamna Zulum hari a duk lokacin da ya yi yunkurin shiga garin Baga domin duba yanayin tsaro da kuma ‘yan gudun hijira a garin da ke dab da tafkin Chadi. Sai dai har yanzu Boko Haram ba ta fito ta dauki alhakin kai harin ba.
Wani mataki kuke ganin ya dace a dauka wurin kawo karshen matsalar tsaro a yankin arewacin kasar nan? Za muso jin ra’ayoyin ku