Borno: Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da mutuwar ƙwararren Soja Kanal D. C. Bako, Kwamandan runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Kakakin rundunar atisayen Lafiya Dole Ado Isa, ya ce Kanal Bako ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagarsa harin kwanton bauna yayin da suka fita sintiri.

A cikin jawabin da Isa ya fitar ranar Litinin, ya ce Kanal Bako ya rasu a asibiti duk da ya fara nuna alamun farfadowa bayan harin ‘yan ta’addar. Sai dai, Isa bai yi karin bayani a kan adadin sauran dakarun soji da su ka mutu ko suka samu raunuka yayin harin kwanton baunar da aka kaiwa tawagar sojojin ba.

“Rundunar atisayen Lafiya Dole ta rasa jarumi, daya daga gwarazanta na yaki, Kanal DC Bako. “A matsayinsa na kwamanda, kullum shine a gaba idan rundunarsa za ta fita aiki.

“Da irin wannan salon jarumta ne ya jagoranci rundunarsa zuwa yankin Sabon Gari – Wajiroko a Damboa domin kawar da sauran mayakan kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

“Dakarun soji, a karkashin jagorancinsa, sun samu nasarar dakile harin kwanton baunar da aka kai mu su tare da samun nasarar kwace makaman ‘yan ta’adda.

“Sai dai, abin takaicin shine Kanal Bako ya samu munanan raunuka kasancewar shine a gaba yayin da sojoji ke yin musayar wuta da ‘yan ta’addar da suka kai musu harin kwanton bauna da misalin karfe 10:00 na safiyar Lahadi.

“Kanal Bako ya fara farfadowa a asibiti bayan an yi masa tiyata, har ya samu damar yin Sallah da safiyar Litinin, kafin ya rasu a asibiti.
“Mu na addu’a Allah ya ji kansa,”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply