Borno: Boko Haram Sun Kai Hari Banki

An fafata a tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun soji a Banki, wani gari dake kan iyakar kasar Kamaru da Nijeriya.

An ruwaito cewa dakarun rundunar soji sun samu nasarar dakile harin da aka kai garin Banki da ke karkashin karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Garin Banki, mai nisan kilomita uku kacal daga iyakar Najeriya da kasar Kamaru, ya kasance cibiyar ayyukan kungiyoyin jin kai.

A ‘yan baya bayan nan dai ?ungiyar Boko Haram na ?ara ?yaimi akan hare haren da ta ke kai wa jama’a a yankin Arewa maso Gabas, inda masu fashin ba?in al’amurra ke ganin cewa hakan ba ya rasa nasaba da barazanar da kungiyar ke fuskanta ne daga farmakin dakarun Soji.

Shugaban ?asa Buhari ya bada umarni ga Dakarun Soji cewa su yi dukkanin mai yiyuwa wajen ganin bayan Boko Haram tun bayan mummunan harin da kungiyar ta kai a garin Zabarmari dake ?aramar Hukumar Jere a jihar makon da ya gabata.

Related posts

Leave a Comment