Borno: Boko Haram Sun Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare A ?auyuka

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da sabbin hare-hare a ?auyukan jihar Borno a yayin da ake tsakar gudanar da bikin Kirsimet da na sabuwar Shekara inda suka yi mummunan ta’adi.

Sai dai duk da haka dakarun sojin Najeriya basu yi masu ta dadi ba yayinda suka yi musayar wuta da su na tsawon sa’o’i masu yawa, inda aka raba dare ana ba ta kashi.

Hakan ya tursasa mazauna kauyukan da abun ya shafa tserewa zuwa saman tsaunuka inda suke kallon fafatawar tsakanin dakarun Sojin Najeriya da miyagu ‘yan ta’addan Boko Haram.

Mazauna kauyukan basu da wani zabi da ya wuce tserewa saman tsaunuka sakamakon musayar wuta da aka dunga yi sannan suka nemi mafaka a jejin da ke kusa domin tsira da rayukansu.

Har a lokacin kawo wannan rahoton ana nan ana fafatawa tsakanin dakarun sojin da mayakan a kauyuka uku da ke karamar hukumar Hawul, inda dakarun Sojin suka yi wa ‘yan ta’addan ?ofar raggo gaba ?aya da nufin ?arar da su.

Idan jama’a basu manta ba cewa mayakan Boko Haram a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba sun kai farmaki karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno. Daga cikin garuruwan da abun ya shafa sune, Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro.

A cewar kakakin rundunar sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, rundunar Operation Lafiya Dole na sama sun yi amfani da jirgin yaki wajen fafatawa da maharan. Ya ce: “Jirgin yaki na ta fafatawa da yan ta’addan Boko Haram kuma ana samun gagarumar nasara.

Wani dan kungiyar sa kai ta JTF, Balami Yusuf, ya fada ma manema labarai cewa har yanzu yan ta’addan na kaddamar da hare-hare a wasu kauyukan.
An tattaro cewa hare-haren dakarun sojin saman ya tursasa yan ta’addan tserewa.

A gefe guda, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba. Gwamnan ya je Abuja don aiwatar da wasu jerin ayyuka amma sai ya takaita tafiyar sannan ya koma jiharsa a safiyar ranar Lahadi.

Related posts

Leave a Comment