Borno: Boko Haram Sun Ƙaddamar Da Hari Akan Manoma

Jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar, mayakan na Boko Haram sun afkawa manoman ne yayinda suke tsaka da aiki a kauyen Alau, a Juma’ar da ta gabata, inda suka sace 2 daga cikinsu bayan yiwa wasu 2 kisan gilla, ta hanyar sassara su da wuka.

Babakura Kolo daya daga cikin jami’an tsaron Civilian JTF yace manaoman sun fito ne daga wani sansanin ‘yan gudun hijira dake wajen birnin Maiduguri, inda suke noman.

Akalla mutane miliyan 2 rikicin Boko Haram ya raba muhallansu cikin shekaru 10, inda mafi akasarinsu a yanzu ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da suka dogara wajen samun tallafin kayayyakin abinci da magunguna daga hukumomin agaji.

Yanayin da aka shiga ya sanya wasu daga ‘yan gudun hijirar rungumar sana’o’in noma da saran itace a dazukan dake zagaye da birnin Maiduguri, domin samun abinci.

A ‘yan watannin baya bayan ne kuma mayakan Boko Haram suka maida hankali wajen kai farmaki kan manoma, makiyaya, masu sana’ar kamun kifi da kuma ‘yan kasuwa, bisa zarginsu da yiwa jami’an tsaro leken asiri.

Labarai Makamanta

Leave a Reply